Hausa News

Al’ummar da basu yarda sarkinsu zai taɓa mutuwa ba a rayuwa

Al’ummar da basu yarda sarkinsu zai taɓa mutuwa ba a rayuwa

Ga mutanen Mankon da ke arewa maso yammacin Kamaru,

sarkinsu wanda aka fi sani da fon ko kuma fo, suna cewa ba ya mutuwa.

Kawai yana ɓacewa ne.

Gwamnan yankin, Adolphe Lele ya gamu da fushin mutanen Mankon bayan da ya sanar da batun mutuwar sarkin mai shekara 97,

wato Fon Angwafor III a ƙarshen makon da ya gabata.

“Sarkin shinne ke da duka ƙasar Mankon.

Shine uban al’adunmu. Kuma shine ƙarshen tsaunin ruhinmu.

Shine tsani tsakanin shekarun baya da yanzu da nan gaba,” in ji Barrista Joseph Fru Awah, wanda sananne ne a Mankon.

Bayan sarkin ya hau kankaragar mulki a 1959, Fon Angwafor III shine sarkin Mankon na farko da ya soma samun karatun boko.

Ya yi karatu ne a lokutan da ‘ya’yan sarki ba su zama a cikin aji domin kare su daga wani baƙon abu da ake kallo na talakawa ne.

Ya ci gaba da karatunsa bayan ya cancanci zama ƙwararre a harkar noma a ƙasar,

don noma ya kasance ɗaya daga cikin abubuwan da mutanen ƙasar suke yi a kullum.

Kamar duka sarakan Mankon, ya kasance mai auren mace fiye da ɗaya ne,

kuma kamar yadda al’adarsu ta tanada, adadin matan da ya aura ba za’a taɓa faɗinsu ba.

Sai dai a ce yana da mata kamar 12, zai iya zama wani hasashe ne kawai.

Haka kuma ana kyautata zaton ya bar gomman yara.

“A kullum yana magana ne kamar wani malami. A duk lokacin da na haɗu da shi, ina tafiya da abinci cikin anashuwa,” in ji Eveline Fung, wadda ta haɗu da sarkin a lokuta da dama.

Sai dai akwai wasu masu caccakar sarkin a lokacin da aka kammala mulkin mallaka a shekarun 1960,

yana daga cikin waɗanda suka tsara haɗe yankunan da Turawan Faransa da na Ingila suka mulka domin zama ƙasar da ake kira Kamaru a halin yanzu.

Mankon na ɗaya daga cikin masarautu mafi girma a yankunan rainon Ingila a Kamaru, inda akwai dubu ɗaruruwan jama’ar da ke zaune a wurin.

Jama’ar da ke ta hankoron kafa yankin masu magana da Turancin Ingilishi ba za su taɓa yafe wa Fon Angwafor III ba sakamakon irin goyon bayan da ya bayar domin haɗe ƙasar.

Wani abu da ba a saba gani ba, sarkin ya taɓa zama ɗan majalisa, wanda ya kafa tarihi ta hanyar zama ɗan majalisar Kamaru mai zaman kansa na farko daga 1962 zuwa 1988.

 

A shekarar 1990, sai ya zama mataimakin shugaban jam’iyya mai mulki ta Paul Biya, shugaban Kamaru na yanzu.

 

Ya ci gaba da zama kan wannan kujerar har lokacin da wa’adinsa ya cika.

 

Masu caccakarsa suna ganin cewa a matsayinsa na sarki, bai kamata a ce ya shiga cikin siyasa ba.

Sai dai ya kare matakin da ya ɗauka, inda ya kafe a kan cewa ya shiga siyasa ne domin kawo ci gaba ga kowa da kowa.

Haramtaccen abin da ya jawo zubar da hawaye

Sai da aka shafe tsawon mako uku sa’annan majalisar ƙoli ta naɗa sabon sarki a Masarautar Mankon ta sanar a hukumance da “ɓacewar sarkin.”

Har zuwa lokacin, mutane sun rinƙa raɗe-raɗin cewa kamar akwai matsala a fadar sarki inda suka kasa furta cewa sarkin ma ya “ɓace” – duk da cewa tuni ma aka rufe shi a wani “tsakakakken wuri” da ba a bari jama’a su sani.

Jama’ar Mankon na ganin cewa haramtaccen abu ne a ce an binne sarkinsu.

Bayan an sanar da “ɓacewar sarkin” a ranar 29 ga watan Mayu,

maza basu saka hularsu ba, haka kuma mata ba suje gona domin yin noma ba domin daraja sarkin.

An kai har 7 ga watan Yuni ana zaman makoki inda dubban jama’a suka taru a fadar sarkin mai shekara 300 a Bamenda – birnin da ke da jama’a 500,000 kuma a nan Masarautar Mankon take.

Sai dai babu wanda ya yi kuka. Babban abin kunya ne a yi kuka ga sarkin da ya ɓace.

An jefi sarki da duwatsu

Maza da mata sun saka siket wanda aka yi da busheshen ganyen ayaba da kuma gora.

Saman jikinsu a buɗe yake, sai dai ga matan da suka saka breziya baƙa.

Bayan masu zaɓen sarki sun zaɓe shi, sabon sarkin – wanda ɗa ne ga Fon Angwafor III – ya shiga cikin gidan sarki,

ba tare da takalmi ba kuma bai sanya riga ba sai dai ya saka farin ƙyale wanda ya naɗe ƙugunsa.

Jama’ar da suka taru sai suka rinƙa jifarsa a hankali da ƙananan duwatsu da ganye da ciyawa,

wadda alama ce da ke nuna cewa wannan ne lokaci na ƙarshe da duk wani talaka zai iya taɓa lafiyar jikinsa ko kuma ya masa rashin kunya.

A lokacin da ake jifarsa, sai ya yi gudu ya shiga cikin gidan sarki inda mabiyansa suka yi sauri suka tafi rafi domin wanke tokar da suka shafa a jikinsu.

Sai suka saka kayan gargajiyarsu mafi kyau, ciki har da dogayen riguna ɗinkin hannu da hula kafin suka koma zuwa fadar sarkin.

Wani abin farin ciki ne domin murnar naɗin sabon sarkin da aka yi.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page