Yanda dan sanda ya dirkawa yar kanwarsa ciki
Yanda dan sanda ya dirkawa yar kanwarsa ciki
Hukumar yan sandan Najeriya ta damke wani jami’inta mai mukamin insifekta,
kan zargin yi wa wata ‘yar kanwarsa, ‘yar shekara 15 fyade, da yi mata cikin shege a Jihar Nasarawa.
An kuma kama wasu mutum uku, ciki har da wani likita, dangane da wannan aika-aika.
Kungiyar mata lauyoyi ta Najeriya wato FIDA, wadda ta bankado labarin afkuwar wannan lamari,
ta ce za ta ci gaba da bin diddiƙin batun, har sai ta tabbatar an hukunta duk wanda aka samu da laifi a al’amarin.
Bayanan an tattaro daga harabar hedikwatar rundunar ‘yan sandan Najeriya a Lafiya, babban birnin Jihar Nasarawa,
sun nuna cewa an damke jami’in dan sanda mai mukamin sufeto, wanda ke aiki a sashen tattara bayanan sirri a wannan runduna.
Reshen Jihar Nasarawa na kungiyar mata lauyoyi ta Najeriya ce ta bankado labarin wannan aika-aika, kuma take ta bibiyar lamarin.
Barista Rabi’atu Ibrahim Addra, wadda ita ce shugabar kungiyar FIDA reshen Nasarawa ta bayyana cewa:
tun da farko sun samu rahoto ne daga wata cibiya ta tabbatar da adalci da zaman lafiya inda suka yi masu bayani kan wannan lamari.
“Da muka samu wannan labarin sai mukaje division B, a nan garin Lafiya muka je muka tarar da yan sanda sa’annan aka kama insifekta din da matarsa da dansa,” inji Barista Rabi’atu.
“Sai muka kai yarinyar asibiti aka je aka yi gwaji aka tabbatar tana da ciki wata shida amma kuma an so a zubar da cikin,
Dan da ke cikinta ‘din, ya mutu har kwana uku yana cikinta.
Ta bayyana cewa a rana ta uku ce suka kai ta asibiti inda har ta haifi ‘ya mace wadda tuni ta mutu a ciki inda tace jaririyar har ta soma rubewa.
Barista Rabi’atu tace: yarinyar ta tabbatar cewa dan sandan ne yayi mata ciki,
Inda tace yakan dawo gida da lemu ko wani abin sha, amma ashe yana zuba mata wani magani ne a ciki,
wanda duk lokacin da ta farka daga bacci sai ta ga jikinta duk ya baci da jini.
A cewarta, sai daga baya yarinyar ta ankara ta gano cewa kawunta ne ke kwana da ita.
Barista Rabi’atu Ibrahim Addra tace, kungiyarsu ta FIDA ta lashi takobin yin tsayuwar daka wajen ganin an gurfanar da masu laifi a lamarin, a kuma hukunta su,
domin hakan ya zama wani kakkausan gargadi ga wasu.