yanda kasa taki karban wata mata da ta mutu
Yanda kasa taki karban wata mata da ta mutu
Wata baiwar Allah ce ta rasu, sai akayi mata sutura.
Daganan aka kaita makwancinta wato kabarinta.
Bayan an kaita ne sai kowa ya kasa binneta a cikin kabarin nata.
Mahaifinta, mijinta da danta duk sun kasa binneta a cikin wannan kabarin.
Haka jama’a suka dinga watsewa daya bayan daya daga wannan makabartan.
Kuji abin Alajabi.
‘Danta ne kawai ya rage bai tafinb. Lallai ‘da da uwa sai Allah.
Yaronnan yana tsaye akan gawar mahaifiyarsa, sai cen yaga mutane biyu sun bullo masa sai sukace ya tafi yabar gawar, su zasu rufe, zasu sakata a cikin kabarinta.
Nan yace “zaku rufe?” Sukace eh idan ka tafi kada ka waigo, yace to.
Yaronan sai ya juya yana tafiya zai bar wannan makabarta, yana cikin tafiya sai yaji ‘kara ta ‘karfi.
Juyawan da zaiyi sai yaga wuta ya tashi sama, yaron bai karika wajen ba amma tiririn hutan ne ya tabashi,
Amma da ya tabashi sai da jikinsa ya ‘daddaye.
Haka a dauki yaron zuwa asibiti, ita kuma wannan gawar babu ita. Baa ganta ba kuma a bakin ramin.
Allah kadai yasan me wannan baiwar Allah take aikatawa har aka kasa binneta daga kabarinta.
Wannan lamari sai dai muce Innalillahi wa inna illaihi raj’un!
Ana kyautata cewa wadannan mutane da sukazo wajen wannan mata ba mutane bane.
Anfi kyautatacewa ma mala’iku ne, wanda suka bada labarin sunce “su da kansu sunje asibitin wajen wannan yaron”
Suka ce “gabaki daya jikin wannan yaron ya daddaye ko ina a jikinsa ya salbe, ko awa daya yaron nan bai karaba ya mutu yabar duniya”.
Allah kadai yasan me wannan mata ke aikatawa a gidan dunuya.
Har yau dai ubangiji na nuna mana ishara,
Wallahi muji tsoron Allah, mu koma ga Allah. Musamman ma Mata.
Allah ka bamu ikon tuba kafin mubar duniya, Allah ka gafartama wannan mata da ta rasu.
Wannan labari da ya faru ya kamata yasa ku kara kin duniya da kyale-kyalen da yake cikinta.
Wai shin duk wannan abin badon neman duniya bane?, duniyan ma idan ka sameta anan zaka barta.
Muyi kokarin neman lahirarmu, idanma kayi me kyau don kanka, idanma kayi mare kyau duk kanka.
Babu ruwan ubangiji, harta ibadama idan kayi don kanka ne,
ga duniyanan a shimfide kayi dukkan abin da ranka keso, amma kaji tsoron Allah saboda duk abin daka shuka akwai ranan da zaka girbesa.