Ali artwork madagwal yasha dukan DSS akan maganar ummi rahab
Madagwal and ummi rahab DSS case
Ali artwork madagwal yasha dukan DSS akan maganar ummi rahab, Ali artwork ya Saka Wani video inda yake nuna shatin duka a jikin sa Wanda yake fadin DSS ne sukayi masa wan Nan dukan.
Ga video Nan a kasa ????????
Ali artwork madagwal yace yaje shigar da Kara akan abubuwan da suke faruwa ne tsakanin sa da ummi rahab da sauran wasu mutane Kuma sai reshe ta juye da mujiya.
A batun Ali artwork madagwal yace tabbas shi yasan Yana da gaskiya Kuma kawai sai hukumar DSS taki sauran sa har ta hada mishi da duka inda ya wallafa hotunan nasa da video akan faruwan abin.
Ama dai wasu suna ganin kamar karya ne saboda office na DSS ba wajen wasa bane har da zaije Yana daukan hoto wan Nan yaje Wani waje ne kawai yayi ta daukan hotunan shi don mutane su tausaya masa.