Wasu ‘yan Najeria sun fusata kan kyautar motoci da Buhari ya ba Nijar
Wasu ‘yan Najeria: Manya-manyan martani da shagube kala daban-daban na cigaba da biyo bayan matakin gwamnatin Najeriya na tallafawa makwabciyarta Nijar da motocin da suka kai darajar kusan naira biliyan daya da rabi.
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tace “ta baiwa makwabciyarta motocin goma da zimmar inganta ayyukan tsaro ne.”
Hakan na zuwa ne a lokacin da Najeriyar ke tsaka da nata matsalolin tsaron a kusan kowane sako da lungu.
Ministar Kudi ta Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed, ta fadawa manema labarai ranar Laraba cewa
“an dauki matakin ne saboda taimaka wa Nijar ta inganta tsaron iyakarta da Najeria”.
Kasashen biyu da kuma Kamaru da Chadi, sun hada iyaka a tsakaninsu mai girma sosai kuma dukkansu na fuskantar hare-haren ta Boko Haram da sauran masu ikirarin jihadi.
A cewar ministar: “An dauki lokaci Najeria tana tallafa wa makwabtan tata, musamman ma mafiya kusanci da nufin karfafasu domin su kare kasashensu ta bangaren da ka iya shafar mu.
Kuma ba wannan ne karon farko da Najeria ta taimakawa Nijar ko Kamaru ko Chadi ba.”
Mutane sun gudanar da bincikenan da ya nuna cewa ba wannan ne karon da Najeria ta fara taimakawa makwabtan nata ba kamar yadda Minista Zainab ta fada, amma a yanzu ne abin yafi fitowa fili.
Sanata Shehu Sani ya wallafa shima a shafinsa cewa “Abin tambayar shi ne, yaya akayi ‘yan majalisa basu lsan da batun sayen motocin ba?”