MIYAGUN JARIDU SUNA DAGA CIKIN MATSALAR TSARON NIGERIA
MIYAGUN JARIDU SUNA DAGA CIKIN MATSALAR TSARON NIGERIA
Wasu miyagun jaridu da suka kware a yada labarun karya da cin amanar tsaron Nigeria,
sun yada wani labari na karya
Inda sukace ‘yan ta’addan Boko Haram sun kaddamar da mummunan harin ta’addanci a babban ofishin ‘yan sanda Zone 1 Kano,
Aslo Read: Gomnatin Buhari tayi martani akan barazar sanatocin PDP na tsige buhari akan rashin tsaro
harin da ya lakume rayukan ‘yan sanda a cewar jaridun
Wannan labarin karya ne aka yada domin a tashi hankalin jama’ar Kano,
rundinar ‘yan sanda na Zone 1 Kano sun fitar da sanarwa akan abinda ya faru kamar yadda zaku gani a hoto da muka daura
Abinda ya faru shine, dazu da misalin karfe 11:45 na safe,
wasu motoci guda uku, dayar kirar Toyota Corolla LE,
da wata mota kirar Akura tana da kalar blue,
sun zo wucewa ta gaban get din Ofishin Zone 1 sai aka harba bindiga daga daya daga cikin motocin da suke wucewa
Wannan harbin bindiga da akayi bai raunata wani jami’in dan sanda ba,
mutanen da suke kusa da Zone 1 headquarters ba su ma san cewa wani abu ya faru ba
Amma sai ga wasu miyagun jaridu suna yada labari na karya
wai ‘yan ta’adda sunyi mummunan harin ta’addanci sun kashe ‘yan sanda a Kano,
hakika wannan cin amanar aikin jarida ne
Allah Ya sauwake.