Hausa News
A Lahira Ne Kadai Ba’a Fama Da Rashin Tsaro, Ko A Amurka An Taba Kai Hari A Gidan Yari – Cewar Buhari
Sugaba Buhari, yace “a lahira ne kadai ba’a fama da rashin tsaro, ko a amurka an taba kai hari a gidan yari”
ya bayyana hakan ne ta bakin karamin ministan kwadago Festus Keyamo,
yayin da yake ganawa da manema labarai na Channelstv.
Keyamo ya bayyana hakane domin ya nunawa ‘yan Nigeria irin namijin kokarin da shugaba Buhari yakeyi kan matsalar tsaro,
inda ya bayyana cewar shugaban a tsaye yake domin ganin ya magance matsalar a duk fadin Nijeriya.
“Gwamnatin Buhari ba cewa tayi zata magance matsalar tsaro baki daya ba,
cewa tayi zata yi kokarin ta magance kuma kowa yaga irin namijin kokarin da take yi.”