Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin Pantami
1. Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin Pantami,
domin duba tsarin nan na biyan ma’aikatan gwamnatin tarayya albashi kai tsaye wato IPPIS,
da tsohon tsarin biyan albashin ta hannun ma’aikatar da mutum yake aiki wato GIFMIS,
da kuma TSA asusu na gwamnati tilo da duk wani kudi da hukumomi da ma’aikatu na gwamnati suke karba ko tarawa yake tafiya kai tsaye zuwa aljihun gwamnati, alfanunsu da nakasunsu.
2. Shugabannin majalisun dokoki na jihohin Arewa ‘yan APC, sun kai wa Tinubu ziyara.
3. Kungiyar Kwadago ta kasa ta bukaci Gwamnatin Tarayya tayiwa ma’aikatan gwamnati karin albashi da kashi hamsin cikin dari,
saboda yadda rayuwar ta yi tsada a yanzun komai ya yi tashin gwauron zabi.
4. Kungiyar Miyetti Allah ta kai gwamnan jihar Binuwai Ortom kara kotun duniya mai hukunta manyan laifuka,
saboda shanun Fulani da yake ta kwacewa.
5. A jihar Kwara ‘yan kungiyar yarbawa ta OPC sun yi fada da Fulani Makita ya,
an ka kashe mutum a kalla shida, wasu baa gansu ba har yau, da dama suna asibiti.
6. A jihar Katsina masu fashin jama’a sun cigaba da cin karensu babu babbaka,
musamman a garin Kankiya inda a baya-bayan nan sukayi fashin wata mata da goyonta.
7. A jihar Kaduna sojojin sun kashe wasu ‘yan bindiga a yankin Chikun,
suka karbe makamansu da baburansu.
Sai mutanen KKB su 35 da aka yi fashinsu kwanakin baya, an sako su bayan an biya kudin fansarsu.
8. A jihar Kogi, wani ne ya kashe ‘yar cikinsa,
ya cire wasu sassan jikinta domin ya yi tsafi,
yabinneta a wani rami. Amma ya shiga hannu.
9. A jihar Taraba, mutum goma sha bakwai da ‘yan bindiga suka kashe, aka kai su makwanci.
10. Ma’aikatan hukumar yaɗa labaru ta jihar Kaduna KSMC,
da aka sallama aiki tun wuraren farkon shekarar da ta gabata, ba tare da an biya su hakkokinsu ba,
suna ci gaba da godon a biya su haƙƙoƙin nasu.
11. Da alamun wannan makon za’a warware matsalar yajin aikin da malaman jami’a suka kwashe watanni suna yi.
12. Ana ta murna da sa’ar da wani ya samu ya daba wa Salman Rushdie wuka a lokacin da ya hau wani dandamali zai yi jabawabi a Amurka.
A yanzun haka ansa masa na’urar taimaka wa majinyaci yin numfashi.
Af! Ga wata tsintuwa da na yi a facebook kamar haka:
A kasar FINLAND
1. Duk malamin da zai koyar a firamare wajibi ne ya kasance yana da digiri na biyu.
2. Iyayen yara ne suke da hakkin zaban Hedimasta.
3. Wajibi ne kowane yaro a saya masa Computer, don baa amfani da littafi.
4. Dalibai 20 kadai a kowana Aji.
5. Muhadara 5 kadai kullum.
6. Albashin Malamin Firamare yafi na shugaban ƙasa yawa.
7. Baa jarrabawar karshen zango. Malami yana fitar da sakamakon ɗalibai ne gwargwadon aikin da suka gabatar a zangon karatu.
8. Malamin Firamare yana da KATI na musamman wanda yake amfani da shi wajen siyayya kuma duk abin da ya siya rabin kuɗin zai biya.
Ga malaman firamare na Nijeriya can, musamman na jihar Kaduna, suna cewa garin dadi na nesa, wai ungulu ta leka masai.