YADDA MIJINA YAYI MIN FYADE
YADDA MIJINA YAYI MIN FYADE
Wata mata ta bada labarin abin takaicin da ya faru a kanta Kamar haka.
“bayan munci abinci munyi wanka abun da ya rage min bai wuce bacci ba.
Amma mijina yace saduwa yakeso da muyi, cikin rarrashi na bashi hakuri nace ya bari da safe muyi.
Nan yayi fushi ya fita ya barni nan dakina, banyi tunanin komai ba na kwanta.
ai kuwa take bacci ya dauke ni saboda dama a gajiye nake, dan nasha aikace aikace.
Cikin bacci naji saukar Mari a gigice na farka tsammanina mafarki nake amma sai naga mijina tsaye a kaina.
Kokari nayi na tambayeshi ko me nayi masa amma kafin na rufe baki ya Kara min wani Marin da yafi na farko ma,
“wai bani da right din da in yana son saduwa dani nace masa AA”
Kenan koda bani da lafiya?
ko bana son yi a lokacin?
ko da bana cikin sha’awa bani da right ince masa yayi hakuri da safe mayi saboda ni macece kuma mace ba mutum bace? “a zuciyata nake wannan tunanin”.
Nayi kokarin nayi masa bayani amma ya cigaba da marina saboda haka bani da zabi dole na kare kai dan bazan zuba ido yana dukana haka ba.
Dan haka Nima na Rama, abun da ya Kara fusata shi kenan ya hau dukana ta ko’ina
Nayi iya kokarina na kare kai amma yafi karfina, da karfi ya yage rigar baccin dake jikina.
Ya yunkurin saduwa dani da karfi, bai rabu dani ba sai da ya tabbatar ya samu biyan bukatarsa.
Abune da na kasa yarda ban taba tunani mijina zai iya aikata min wannan ba”
Ko wannan mata tayi kuskure da ta gayawa mijinta yayi hakuri da safe su sadu?? Ko gaskiya ne fyade yayi mata?
Yi comment ka/ki Fadi ra’ayinka a wannan batu………
2 Comments