News

Da Dumi-duminta: Rikice Ya Sake Barkewa A Jam’iyyar PDP

Jam’iyyar PDP, Da Dumi-duminta: Rikice Ya Sake Barkewa A Jam’iyyar PDP

Ko ba Wike zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa, cewar Atiku Abubakar

Rahoton Daily News Hausa

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ganawar da Atiku Abubakar ya yi da gwamnan jihar Ribas,

Nyesom Wike ta gaza kawo wani sauyi a rikicin da ke tsakaninsu.

A cewar rahoton, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya gana da gwamnan a gaban kwamitin amintattu na jam’iyyar (BoT),

karkashin jagorancin Sanata Walid Jibrin.

An ce tsohon ministan yada labarai da al’adu, Farfesa Jerry Gana ne ya shirya taron a gidansa.

A wani taro da mambobin BoT na PDP a ranar Laraba, 3 ga watan Agusta,

Atiku ya bayyana cewa PDP za ta iya lashe zaben badi ba tare da kuri’un jihar Ribas ba.

Ya ce babu wani abin fargaba idan Wike bai so ya goyi bayansa ba a yakin neman zabensa.

Cike da kwarin gwiwa, Atiku ya tuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari,

wanda shi ma bai ci jihar Ribas ba, ya dogara ne da kuri’u daga jihohin Legas,

Kano da sauran jihohin da ya kamata ya lashe zaben shugaban kasa na 2019.

Ya kuma ce PDP ta shiga taskun rikici ne saboda Wike ya sanya batun kudi a zaben fidda gwani na shugaban kasa da aka gudanar.

Me za ku ce?

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page