News

Na sanya hannu kan sanarwar tsige Buhari – dan majalisar wakilai (Reps member)

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jos ta kudu/Jos ta gabas a majalisar wakilai, Dachung Bagos, ya bayyana cewa

“ya sanya hannu kan takardar tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari daga mukaminsa.”

Aslo Read: Nifa Ban Tilastawa Kowa Ya Zabeni Ba Cewar Muhammadu Buhari

Yan Nigeria Kukan dasi Sukeyi

NIGERIA POLITIC ta rawaito cewa Bagos yaKai wannan matakin ne biyo bayan kashe wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka yiwa mazabarsa bakwai a ranar Lahadin da ta gabata.

Kisan dai yazo ne sa’o’i 24 bayan da mutane 18 suka rasa rayukansu a wani rikici tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan banga a karamar hukumar Wase (LGA) ta Jihar Filato.

Bagos, wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin majalisar kan yaki da cin hanci da rashawa,

ya halarci jana’izar mutane bakwai da aka kashe a kauyen Danda a ranar Litinin.

“Wannan lamarin ya tayar da hankalin jama’a kan shirye-shiryen da hukumomin tsaro keyi na magance salon kashe-kashen da ya zama ruwan dare a mazabana da jihar Filato.”

“A matsayina na wakilan jama’ata na mazabar Jos ta kudu/Jos ta gabas a majalisar tarayya,

na sanya hannu kan tsige shugaban kasa saboda muna bukatar wanda zai magance matsalolin rashin tsaro.

Kullum ana kashe mutanena; wannan abin Allah wadai ne kuma ba za a yarda da shi ba,” inji shi. (Dan majalisar wakilai)

Tou Allah kasa mu dace ka kuma bamu shuwagabanni nagari. Ameen

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page