Babu Sakarai Kamar Wanda Zai Zabi Sak A Zaben 2023
Babu Sakarai Kamar Wanda Zai Zabi Sak A Zaben 2023
…Domin jam’iyya ba ita ce matsalar mu ba, lalatattun shuwagabanni sune babbar matsalar mu,
kuma akwaisu a kowace jam’iyya.
Also Read: Nasarawa state: Wani jamiin tsaro ya dirka ma ‘yar Dan uwanshi ciki ‘yar shekara 15
More Garabasan Glo Free Browsing
Ra’ayin Comr Abba Sani Pantami
Babban fatana kafin zaben shekarar 2023, kowane dan Najeriya ya fahimci jam’iya ba ita ce matsalar mu ba,
lalatattun shuwagabanni sune babbar matsalar mu, kuma akwaisu a kowace jam’iyya, kusan ma sune suka fi yawa.
Babu sakarai kamar wanda zai zabi sakkk a zaben shekarar 2023,
domin babu wani irin darasin rayuwa game da ‘yan siyasa wanda bamu gani ba,
babu wani abu game da halayyar ‘yan siyasa wanda bamu gani ba,
ya kamata tuntuni mu dau haske akan duk wata halayya tasu.
Domin idan muka yadda muka sakeyin wani kuskuren to tabbas za’a koma inda aka baro ko a kara fadawa inda ma bamu kai ba.
Idan muka kula, mafi yawan wa ‘yanda ke jam’iyyar APC yau wata rana a baya sune a jam’iyyar PDP ko wasu jam’iyu,
bukatun kansu ne suka kawo su APC, ko kuma suka kaisu wasu jamiyyun.
Mafitar mu shine na farko mu koma ga Allah,
na biyu mu kauda kai daga batun jam’iyya, duk inda muka ga mutumin kirki kawai mu zabe shi. (Sak)
Duk da munsan samun mutanan kirki yana da matukar wahala,
amma ana samun dama-dama, hausawa suka ce da baki wuluk kwanda baki-baki.
Inkunne yaji, gangar jiki ta tsira.
Allah ka bamu shugabanni Nagari koda bamu son su, matukar zasu kwatanta Adalci akan mu.
Allah ya kawo mana karshen matsalar rashin tsaron da ya addabi yankin mu na Arewa dama kasar Najeriya baki daya.
Amin!