Hausa Series

An Kama Matsafa Da Gawawwaki Ashirin

An Kama Matsafa Da Gawawwaki Ashirin

Rundunar ‘yan Sandan jihar Edo ta kama wasu mutum uku a wani dakin tsafi dauke da tsofaffin gawawwaki ashirin da aka busar dasu za’ayi tsafi.

Rundunar ta bayyana hakan ne ranar Alhamis a Benin, babban birnin jihar cikin wata sanarwa da ta fitar ta bakin mataimakin Kakakinta, ASP Jennifer Iwegbu.

Jennifer tace “an gano gawawwakin ne a wani gida da ke unguwar Asoro da ke birnin na Benin.”

Ta kara da cewa, “Biyo bayan wasu bayanan sirri da muka samu cewa an gano wasu gawawwaki a unguwar Asoro,

mun tura tawagarmu cikin gaggawa unguwar da aka sanar damu ana tafka wannan aiki,

kuma mun samu nasarar kamo mutane uku a gidan bayan munje, yayin da sauran suka tsere.

Amma hukumar ‘yan sanda bazata kyalesu ba zata binciko su tayi musu hukunci dai dai dasu.

“Baya ga haka kuma, mun gano gawawwakin maza 15 da suma aka busar, da na mata uku,

sai kuma na kananan yara biyu.”

“Ganin haka Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Abutu Yaro,

ya bawa Mataimakinsa na sashin binciken sirri umarnin binciko musabbabin mutuwar gawarwakin,” inji ta.

Jennifer ta kuma ce al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu,

domin zasu cigaba da tabbatar da sun kiyaye rayuka da dukiyoyin su kamar dai yadda doka ta dora musu.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page