Hausa Series

Labarin Wata Mata: Na Kama Mijina Da Wata Matar Aure

Labarin Wata Mata: Yanzu Haka Zuciyata Tafarfasa Kawai Take Saboda Na Kama Mijina Da Wata Matar Aure

Dazu na dawo daga unguwa sai naga mijina ya dauko budurwarsa a mashin suna tafiya suna hira suna murmushi,

tun daga nesa bai ganni ba, amma ni na ganshi.

Sai da yazo gab da ni muka hada ido da shi yaga na hade rai,

yazo gabana ya tsaya cikin sakin fuska da murmushi, sai cewa yayi sannu Auntynmu ina zakije ne haka kike faman sauri? Sai yace da budurwasa ki gaishe da ita matar dan uwanata ce,

ita kuma har tana gaishe da ni saboda bata san ni matarsa ba ce.

Tsabar bakin ciki da takaici na rasa abinda zance,

kawai nayi gaba na tafi na barsu a wajan shima yaja mashin ɗinsa suka tafi.

Yanzu na dawo gida ko abinci na kasa ci saboda bakin ciki da takaicin abinda ya min,

saboda cin fuska ba zai iya fadawa budurwarsa ni matarsa bace saboda kada ranta ya baci har da cewa ni Antynsa ce.

Saboda haka nake neman shawararku, wanne irin mataki ya kamata na dauka idan ya dawo tunkun kafin inyi anyen aiki.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page