Yanda Ake Lalata Mata Masu Tallah
Yanda Ake Lalata Mata Masu Tallah
Sau tari ‘yan mata masu talla na karewa ne da tallata kansu a maimakon kayan da suka dauko talla.
Wata budurwa ta kako akan tana sayar da ruwa amma baza na damunta.
Ina Tallan Pure Water Amma Maza Sun Dame Ni Da Karbar Lamabar Wayata Akan Titi
Sana’ar sayar da ruwan leda da a ke kira da ‘Pure Water’ da ruwan roba wato ‘Bottled Water’
da ma sauran nau’ikan lemuka na kan tituna ya zama ruwan dare gama duniya.
sakamakon karbuwan da sana’ar ta samu a matsayin hanyar samun taro da kobo ga masu yinta
da kuma taimakawa masu zirga-zirga a ababen hawa da ma a kasa domin samun abin jika makoshi a lokacin da bukatar hakan ta kama.
Wata zukekiyar budurwa mai sayar da ruwa a Accra babban birnin kasar Ghana
ta koka kan yadda maza ke tsayar da ita amma ba don su sayi ruwa ko lemon da ta ke talla ba,
a’a, sai kawai don su karbi lambar wayarta da nufin su kirata bayan ta gama tallan don su fahimci juna wajen lalata.
Sai dai kuma wannan mai sai da ruwa ba wata bace illa fitacciyar mawakiyar kasar na ghana,
Wato Nina Ricchie, nina tayi ‘bad da kama a wani salo na yaki da munanan dabi’u a cikin al’umma,
musamman ta’adar dora talla ga ‘yan mata,
Nina ta dora a shafinta na Instagram,
yadda ta sha fama da samari a dan fita da tayi tallan na dan sa’o’i kadan,
inda tayi kokarin bayyanawa iyaye irin hadarin da ‘ya’ya mata suke fuskanta a lokacin da suka fita talla.
Sau tari ‘yan mata masu talla na karewa ne da tallata kansu a maimakon kayan da suka dauko talla.
Abun haushinma shine wasuma yara qana ne wanda basu gama sanin komi na rayuwa ba.
Wasu dalilin hakan suke gani da sun sama abin da suke so s saukake wajen yin lalata dasu.
A gaskia wannan ya balagazar da mace, yasa bazaaga girmanta ba dana iyayen da suka daura mata.
Tou iyaye kunji matsallar da ake fuskanta kan faurawa mace talla. Sai a kiyaye.