Sau shida kacal na taba lalata da ita, a cewarshi
Sau shida kacal na taba lalata da yarinyar, mahaifiyarta ce ke zuzutawa – Wanda ake zargi
Wani mutum mai shekaru 40 mai suna Edet Imoh,
ya amsa laifin da ake zarginsa a gaban ‘yan sandan jihar Legas.
Ya tabbatar da cewa yayi lalata da diyar makwabcinsa mai shekaru 11
“amma sau shida kacal ba kamar yadda mahaifiyar yarinyar ke cewa da yawa ba”.
‘Yan sanda sun kama Imoh wanda ke zaune a titi daya da mahaifan yarinyar a titin Oyekanle da ke Bariga da ke tsakiyar birnin Legas,
bayan rahoton da mahaifiyar yarinyar ta kai wa ofishin ‘yan sanda da ke Bariga.
An zargi cewa, a duk lokacin da wanda ake zargin ke son lalata da yarinyar,
zai kirata dakinsa a kan cewa zai aiketa siyo wani abu.
Asiri ya tonu bayan da wani makwabcinsu ya lura da hakan tare da sanar da mahaifiyar yarinyar yayin da take neman diyarta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, ya ce “an kama wanda ake zargi wando a kasa yayin da karamar yarinyar ke kwance yana lalata da ita.
“A yayin da aka tambayeshi yayi bayanin abinda ya faru sai yace aikin shaidan ne.
Ya ce sau shida kacal ya taba lalata da yarinyar ba sau da yawa ba da mahaifiyarta ke ikirari.”