Wani Magidanci Ya Dirkawa ‘yar Kanin Shi Cikin Shege
Wani Magidanci Ya Bawa Matarshi Hakuri, Bayan Ya Dirkawa ‘yar Kanin Shi Cikin Shege
Majiyarmu ta samu wani labari cewa wani magidanci da yaima ‘yar kaninshi cikin shege wanda abun baiyi dadi ba ga, yadda takasance.
“Wani magidanci dake zaune a karamar hukuman Dala dake jahar Kano, ya dirkawa wata marainiya wacce take matsayin ‘ya a gurinshi ciki,
wacce yarinyar tana da kimanin shekara shabiyar a duniya, inda ya ribaceta da lemun kwalba.
An ruwaito cewa kafin ya bata lemun sai da ya saka kwaya aciki sannan ya bata, nan take ta kama bacci shi kuwa ya afka mata.
Bayan sati Biyu da faruwan lamarin matarsa wacce take rike da yarinyar, ta fara ganin wasu alamu a tattare da yarinyar,
inda ta garzaya asibiti da yarinyar don yi mata gwaji, anan ne aka tabbatar mata da ‘yarta tana da juna biyu inda suka takura yarinyar ta fada, sai ta amsa da cewa Baba ne.
Magidancin ya shaidawa matar tashi cewa tayi hakuri lallai shedan ne ya ribance shi kuma hakan bazata sake aukuwa ba.