ABACHA BA BARAWO BA NE, GWARZON SHUGABA NE, KUMA JARUMI NE
ABACHA BA BARAWO BA NE, GWARZON SHUGABA NE, KUMA JARUMI NE
Da yawa daga cikin ‘Yan Nigeria an sanya musu a zuciyar su cewa:
Tsohon Shugaban Nigeria Marigayi Gen. Sani Abacha Barawo ne.
Wannan Tunani ne da wasu daga cikin Manyan Jagororin Nigeria,
tare da hadin Gwuiwar wasu Manyan Kasashen Gabas suka kirkira domin cimma Bukatun su na Siyasa ko kuma Tattalin Arzuki.
Irin wadannan Jagorori da babu abunda suke a kullum banda kokarin kawo cikas ga cigaban Nigeria
da zaman lafiyar Kasar sune kan gaba wajen kiran Abacha da sunan Barawo
tare da taimakon wasu Kafafan Sadarwar da suke yada abun don Kabilanci.
Marigayi Gen. Sani Abacha yana daga cikin Shugabannin Nigeria wanda Kasar ba zata taba mantawa da Alkairan su ba.
Abacha Jagora ne wanda irinsa ne Kasar take bukata domin inganta lamuranta gida da waje,
domin shine shugaban da ya dora Nigeria akan Hanyar da Kasar zata Bunkasa.
Abacha ya inganta Tattalin Arzukin Nigeria wanda kusan ana iya cewa babu wani Shugaba da yayi irinsa a Tarihin Nigeria.
Daga Shekarar 1993 zuwa Tsakiyar 1997 Abacha ya daga Asusun ajiyar Nigeria na Ketare,
daga Dalar Amurka Miliyan 494 zuwa Dala Biliyan 9.6, ya rubanya shi da kusan kaso 90%.
Har ila yau Abacha ne shugaban da ya rage yawan Basukan da Kasashen Waje ke bin Nigeria
daga Dalar Amurka Biliyan 36 zuwa Dala Biliyan 27 abunda ya kara tayar da hankulan Kasashen Gabas
domin ganin cewa Abacha ya hau layin Yantar da Nigeria ne daga Mulkin Malakarsu.
General Sani Abacha
Abacha ya rage yawan hauhawar Farashi a Nigeria daga kaso 54% da ya gada daga Tsohon Shugaba Ernest Shonekan zwa 8.5% tsakanin 1993 – 1998.
Baya ga haka, Abacha ya samar da Tituna masu tsahon 25-109 KM a mafiyawancin Biranan Nigeria irin su Zaria, Kano, Enugu, Benin, Gusau, Funtua, Kaduna, Port Harcourt, Lagos, Lakoja da sauran su.
Abacha ne ya samar da Hukumar PTF wacce ta samar da manyan ayyukan cigaba a fadin Nigeria Lungu da Sako na Kasar wanda har ya zuwa yanzu Yan Nigeria na amfana da ayyukan wannan Hukuma wacce Abacha ya nada Shugaban Nigeria Muhammad Buhari domin ya Jagoranta.
Irin wannan ayyuka da Abacha ya kewa Nigeria ne ya sanya Kasashen Gabas yin gaba da shi tare da kokarin ganin bayansa ta hanyoyi daban-daban wanda ya hada da taimakon wasu marasa kishin Nigeria.
Anyi amfani da wasu Jaridu masu kokarin yada Kabilanci domin bata sunan Abacha wanda wasu lalatattun Shugabanin Nigeria ke daukar nauyi.
Hakik rashin karanta tarishi na daya daga cikin babban matsalar mu a yau.
Allah ya jiqan Abacha yayi Rahma gare shi, Amin.