Allah Ne Kadai Ke Da Ikon Dauke Mana Dukkanin Bukatunmu Ba Buhari Ba
Allah Ne Kadai Ke Da Ikon Dauke Mana Dukkanin Bukatunmu,
Don Haka Shugaba Buhari Ba Shi Da Alhakin Dukkan Matsalolin Dake Addabar Nijeriya
Da a ce dukkan mutane zasu taru don su cuce ka, to ba zasu cuceka da komai ba,
haka kuma da dukkan mutane zasu taru don su amfane ka bazasu amfane ka da komai ba, sai abunda Allah ya rubuta maka.
Duk abunda ka ga ya same ka, to dama Allah ya yi ba zai kuskure maka ba.
Ya kamata mutane muyi tunani mu daina zagin Shugabbanni, basu ke da alhakin dukkan abunda ke faruwa da damun mu a yanzu ba,
muji tsoron Allah mu gyara halayenmu, mu yawaita addu’a, Allah ya kawo mana sauki cikin dukkan lammuranmu,
Shugaba Buhari bashida alhakin dukkan abunda yake damun mu, kama daga na ci, sha, lafiya, tsaro da dai sauransu.
Allah kadai ke da ikon dauke mana dukkan bukatunmu ba Shugaba Buhari ba,
mu koma ga Allah, mu gyara halayenmu, mu daina zagin shugabanni da tsine musu.
Yau ko akwai Shugaba Buhari ko babu shi, idan Allah ya rubuta za mu sha wahala to tabbas za mu sha shi.
Allah ya taimaki Shugabannin mu, Ya idda musu manufofinsu na alkairi a gare mu,
Allah ya kyautata karshenmu, ya kawo mana sauki cikin dukkan lammuranmu.
Zabe mai zuwa Allah ya baiwa wanda shine mafi alkairi a gare mu baki daya.
Allah ya sa mu dace. Amin.