Health

Maganin basir: Matsalar rashin sha’awa ga mata da miji

Maganin basir: Masu aure ya kamata ku sani ko Kuma nace ku Kara tinawa matsalar basir babban illa ce wajen mace Dana miji gaba daya,

Yana dauke sha’awa gaba daya mace Kona Miji Basu sha’awa na junan su,

yakan Saka azzakarin namiji taki tashi ko ta koma karama,

ko Kuna fara saduwa kuji Kun gaji,

babbar matsalar ma Koda sunyi jima’i ba zasuji Dadi sosai ba saboda matsalar basir,

don haka Yana da mahimmanci akoda yaushe ku dinga service na jikinku da magani Wanda bazai muku illa ba.

Ku tabbatar da kuna shan maganin basir bawai sosai ba, kuyi ta banka ma kanku maganin dazai cutar daku,

A’a ku dinga shansa lokaci bayan lokaci misali sau hudu, sau uku ko sau biyu a duk wata,

ya danganta ne da irin inda basir din kuke jinsa a jikin ku. (Maganin basir)

Basir kala-kala ne

  • Basir me tsiro.
  • Akwai me kumbura ciki.
  • Yawan Saka Hutu (tusa).
  • Me tsatsaga dubura.
  • Da akwai mesa bahaya yayi karfi sosai yayi tauri.
  • Akwai me Saka kaikatin dubura, akwai Mai Saka bahaya da jini.

Kadan daga alamomin basir da zaku iya ji acikin jikinku sune kamar haka:

  • Yawan yin tusa, yawan Jin kaikayi a dubura,
  • Dubura ta kumbura kota zazzago, yawan Jin kasala ko bacci,
  • Ana Kashi ana Jin zafi saboda yayi karfi Yana fita curi curi,
  • Mutum yaji duburan shi ya tsatsage Yana mishi zafi kamar an zuba barkonu,
  • Yana Saka ciwon baya,
  • ko ciwon gabobi.

Kadan daga maganin ko nace Riga kafin ciwon basir shine,

duk Wani Abu me bauri ko dauri ko daci Yana iya maganin basir ko Kuma rigakafin sa,

amma fa akiyaye asha da lura saboda matsalar hanta ko Koda.

Ga masu basir me tsiro ko Wanda ya tsatsage ko me kaikayi,

ku samu man habbatusauda, da man tafarnuwa da man zaitun.ku hada shi ku dinga sawa a diburanku musamman idan zaku kwanta Koda safe kafin ku shiga wanka.

Zaku iya karanta: Wani me gida yayi lalata da wata mace da karfi

Haka Nan zaku iya samun sassaken mangwaro sassaken baure, Dana kadanya,

a hada su a dafa adan saka musu jar kanwa kadan aciki a dafa a dinga sha kulum sau daya ko sau biyu a Rana,

ga masu me tsiro ko tsatsage wa sai su dinga sashi yayi dumi su dinga shiga cikin shi kulum safe da dare amma sai ansa shi yayi dumi.

Ga Wanda basir yake dauke mishi sha’awa ya Hana azzakarin shi taki tashi, a nema abubuwa kamar haka:

Kanemi sassaken dinya da saiwar tsada da saiwar sabara,

amma yakamata sassaken dinyar yafi yawa sosai,

sai a dakasu sai a gauraya waje guda,

kulum a dinga dafawa kamar Kofi Daya ana sha kulum bawai dole sai anshanye Lokaci Daya ba.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page