Wasu Sirrukan Mata Guda 10 Da Ba Duk Maza Suka Sansu Ba
Mata wasu halittune na musamman da idan banda wanda ya haliccesu babu wanda zai iya ce maka yasansu cikinsu da bayansu.
Wannan rashin sanin nasu ko fahimtarsu ne yasa wasu mazan bama sa iya zama inuwa guda da mace. Duk mutumin da zai ce maka ya karanci halayen mata 100 bisa 100, wannan mutumin son ransa ne ya fada amma ba gaskiya bane. Ita mace komai girmanta da kankantar ta sai Allah.
Ga wasu Sirrukan Mata da akasarin maza basu sansu ba:
1: Duk maganar da mace zata fadamaka cikin fushi ba dagaske take yi ba. Bakamar namiji ba. Abunda zai fadamaka yana fushi ko ya huce zai iya maimaita maka.
Wasu mazan da zaran sunji mace na cewa a saketa, ko ta tsaneshi. Ko bata sonshi sai ya zaci abunda take cewa har zuci ne. Sai ya biye mata daga baya kuma ta dawo tana bashi hakuri.
Idan mace ta soma yi maka bakaken maganganu a lokacin da ranta ya baci. Rungumo kayanka kana shafata kana bata hakuri kana rarrashinta. Idan ma da sarari kwabeta, nan take zaka ji ta tsit.
Da kuma bakuyi aure ba. Ka cikata da dadin baki ko kuma ka tashi ka bar wajen.
2: Maza da dama basuda masaniyan cewa, babu lokaci mafi tashin hankali wajen mace kamar lokacin da tayi nisa da wanda take sonsa da gaske.
Mace idan tana son namiji batason ganin ya taka kafa daya ba tare da ita ba. Amma saboda yanayin aiki ko kasuwanci yasa suke hakuri amma ba domin zuciyarsu na son hakan ba.
Yana da kyau maza su sani idan kayi nisa da wacce take sonka. Ya kamata ka kusanceta ta hanyar sadarwan na zamani ta rika ganin tamkar kana kusa da ita.
Wannan wani sirri mata ne da maza da dama basu sanshi ba.
3: Mace takan dauki lokaci kamin ta amincewa namiji. Amma kuma daga lokacin da ta amince masa zata mika masa wuya sai kuma yadda yayi da ita. Hakan ne yasa wasu mazan da zaran sun samu mace cikin sauki sai su rika mata kallon mara daraja. Wannan ne kuma yasa sai mace ta gama jan ajin nata kaf, daga baya kuma ta fada hannun namijin yayi ta gallaza mata saboda yadda ta dawo take sonshi.
4: Kamar yadda nayi bayani a baya. Mace wata makarantace da babu ranar da namiji zai iya kammala karatunta. Don haka ajiye girman kanka ka dauki darasi daga duk wata macen da zaka hadu da ita.
5: Ita mace a kullum tana tafiya ne da alfanunta da kuma sharrinta.
Duk yadda mace ke sonka sai ta bata maka rai. Haka duk yadda take kinka akwai ranar da zata dadadamaka. Don haka ita mace zuma ce.
6: Mace tana saurin manta alheri. Amma komai tsufan mace bazata taba manta abunda aka yi mata na rashin kyautawa ba. Don haka idan zaka yi mu’amala da mata kayi shi cikin girmamawa.
7: Mace tana da tsoron Allah a zahiri. Amma bata gudun azaba akan duk wani abunda zata yi idan ranta yana son wannan abun komai muninsa.
8: Mace tana da saurin tausayawa da taimakawa. Sannan tana da sauri gorantawa.
9:Mace takan rike sirri ne idan tasan tona asirin abun zai shafeta. Muddin tasan sirrin da aka bata ba wanda zai zubar mata da mutunci bane, cikin sauki zata fadawa wasu tace musu ita sirri ne aka bata suma ta basu sirri.
10: Mata tamkar gishiri suke. Idan suna waje ba lalle bane a fahimci hakan. Amma idan har babu su a waje kowa sai ya fahimci babu su.
Matan mutanen mu. Mata iyayen mu. Mata Kayan marmarin mu. Duk wanda yazo duniya ta hanyarku yazo. Wanda ya iya daku ya huta. Wanda ya ce babu ruwansa daku ya shiga wahala.