Sojan Rasha zasu Bada ajiyar Ruwan maniyi nasu a ajiye a asibiti
Sojan Rasha zasu Bada ajiyar Ruwan maniyi nasu a ajiye a asibiti.
Gwamnatin kasar Rasha tayi gangami na diban sabbin soja saboda yakin da sukeyi da yukurain Hakan yasa an kashe musu sojan su da yawa wasu Kuma sun samu rauni.
Hakan yasa suka Kara diban sabbin yara masu jini a jika domin aci gaba da fafatawa daga inda aka tsaya.
Hakan yasa suka bawa sojan kasar na Rasha dama ga duk me bukata ya Bada ruwan maniyi nashi a daskarar dashi a ajiye mishi a asibitin kasar.
Hakan shine zai bawa matan su Daman Kara anfani da wan Nan ruwan maniyi su iya Kara haihuwa Koda bayan sun mutu ko Kuma sun samu matsala na Dena haihuwa a fagen yaki.
Duk da Hakan wasu zasu iya ganin shi a sabon Salo ko Kuma wani Abu mare yuwuwa.
Amma ilimi ne ya wuce duk inda mutane Suke tinani Hakan an dade ana yinsa, idan mace tana da bukatar haihuwan namiji ko Kuma mace ko tagwaye, sai taje asibiti suba mata maniyi dai-dai da bukatar ta.