yan majalisa sun umurci jami’an tsaro su kama mutum 54 a gwamnatin buhari bayan binciken kudi
kwamiti yan majalisa dake binciken wasu daga cikin ma’aikata a nigeria ya bukata da jami’an tsaro da EFCC dasu kama wasu manyan ma’aikata da directoci saboda zamba da almundahana da kuma rashin bada cikaken bayani akan inda suka kashe kudaden su da gwamnati ta basu.
shugaban kwamitin, Hon. Oluwole Oke ya sanar da hakan ne a daren juma’a inda yake nuna sun gayyata shugabbani da sauran manyan maaikatun gwamnati da directoci domin suzo majalisa suyi bayan akan kudaden da suka kashe amma sukaki zuwa.
sabuwar hanyar da masu garkuwa da mutane suka dauka saboda canjin kudi
yan majalisa sunce don mun nema da a bamu bayani akan kudaden da aka kashe a tsakanin 2014-2018 da kuma 2019-2021 a maaikatun kasar nan da abin ya shafa amma sun hana mu a rubuce kuma sunki zuwa su kare kansu.
kadan daga cikin mutanen da aka umurci jamian tsaro dasu kamasu sune kamar haka, gwamnan babban banki na kasa watau CBN, Mr. Godwin Emefiele.
Haka nan ana neman manyan shugabannin kamfanin mai na kasa (NNPC), tare da hukumar kula da cigaban Neja-Delta (NDDC) da RMAFC ta fannin biyan albashin ma’aikata na kasa.
majalisa tace 89(d) na kundin tsarin mulki ya bada daman susa jamian tsaro dasu kama wadanda ake zargi nan da sati daya