Borno state: wasu manyan Nigeria sun nema afuwa ga marayun da aka kashe iyayen su a borno
Borno state
Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya nema da marayun da aka kashe musu iyaye a borno state dasu yafe ma yantaada.
Hakan ya biyo baya ne bayan zuwan Obasanjo Wani makaranta marayu a garin borno state, inda ya nema Yara marayu dasu yafe ma yantaada Wanda suka kashe musu iyaye.
Ya fada musu Hakan ne acewar sa domin su mayar da hankalin su a wajen karatu saboda abinda ya Riga ya faru ya wuce bazai Kara dawo wa ba don haka su manta da komai suci gaba da mayar da hankalin su akan karatu.
Obasanjo ya Kara da cewa wan Nan malaman naku sune iyayen ku don haka ku Dena damuwa da rashin iyayen ku zasuyi muku komai a rayuwa kamar inda iyayen ku zasuyi muku.
Obasanjo ya samu raddi kala-kala daga mutane akan wan Nan kalamai nashi, domin duk Wanda aka kashe mishi iyaye akan idon sa ace ya manta da Hakan Abu ne me wuya.