Shugaban kasa Muhammad buhari ya karya tatalin arzikin Nigeria inji sunusi lamido sunusi
Sunusi lamido sunusi yace shugaban kasa Muhammad buhari shine matsalar Nigeria Kuma shine Wanda ya karya tatalin arzikin Nigeria.
A Wani taro da akayi a garin legas me girma sunusi na biyu ya zargi wan Nan gomnatin na Muhammad buhari da karya tatalin arzikin Nigeria.
Kamar inda sunusi nanbiyu ya fada cewa tin farkon hawan mulkin su a shekaran 2015/2016 ya fada ma shugaban kasa Muhammad buhari cewa wan Nan akida da suka dakko dashi da mutanen sa zai Saka Nigeria da mutanen cikinta cikin mawuyacin hali.
Shugaban kasa Muhammad buhari yayi yayi Kunin Kashi yayi bursu da wan Nan Shawara da tsohon gwamnan banki sunusi l sunusi ya kawo masa.
Sunusi lamido yace be Gaza ba yaci gaba da tinasar dashi har da tura mishi wasikar sirri da Gane da irin mawuyacin halin da Nigeria ke Shirin fadawa amma Ba’a saurara maganar sa ba.
Sunusi lamido sunusi yaci gaba da cewa tabbas Nigeria da mutanen ta suna cikin mawuyacin hali Wanda Allah ne kawai zai fitar damu.
Sunusi lamido yace indai har ba za’a Dena San Rai na Mulki a kasar Nan ba ya kasance shugaban kasa gomna ministoci kowa ya Dena San kanshi a koma yin abinda ya kamata to Babu ranar da wan Nan kasa zata koma dai dai.
Haka Nan Yana kira ga matasa kowa ya kasance me Neman na kanshi Kuma mu Dena zaben shugabanni saboda kudi ko Wani Abu mu koma zaben su ne saboda aikin da zasuyi mana.