Isa Ali Ibrahim Pantami: Ministan Sadarwa Farfesa Isa Ali Pantami Ya Samu Matsayin Da Babu Wani Mahaluki Da Ya Taba Samu A Africa
Isa Ali Ibrahim Pantami, DA DUMI-DUMINSA: Ministan Sadarwa Farfesa Isa Ali Pantami Ya Samu Matsayin Da Babu Wani Mahaluki Da Ya Taba Samu A Afrika
A duk fadin Duniya masu shaidar CIISec ba su kai mutum 100 ba,
Farfesa Pantami ne mutumin farko da ya fito daga kasashen Afrika.
Rahoton Daily News Hausa (Isa Ali Ibrahim Pantami)
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani,
Isa Ali (Pantami) ya samu lambar zama ‘dan kungiyar Chartered Institute of Information Security.
Farfesa Isah Ali (Pantami)
Farfesa Isa Ali (Pantami) ya samu wannan lamba ne biyo bayan wasu jarrabawowi da kungiyar tayi wa Mai girma Minista.
Kamar yadda cibiyar mai bada lambar girman ta bayyana,
ana bada CIISec ne ga jagororin da suka yi fice wajen harkar tsaron bayanai da kafofin yanar gizo a Duniya.
Pantami ya zama dan Afirka na farko na CIISec
BAYAN SANARWA, Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Dijital, Farfesa Isa Ali (Pantami).
Ya sami matsayin hadin gwuiwa ta Cibiyar Tsaron Bayanai ta Chartered, CIISec.
An karrama ministan ne bayan tattaunawa da kuma tantancewa, tare da lambar yabo,
Pantami ya zama na farko kuma dan Afirca tilo da aka shigar dashi cikin CIISec, a tsakanin sauran abokan 89.
Tambaya
Wane fata za ku mishi?