Bola tinibu ya ziyarci Nasiru Elrufa’i kaduna
Me neman takaran shugabancin kasa na Nigeria Bola tinibu ya ziyarci Nasiru Elrufa’i kaduna yau talata 5 April 2022.
Bola tinibu ya ziyarci kaduna a yau domin jajanta ma mutanen kaduna saboda faruwan fashewan jirgin kasa da aka samu wasu suka raunata wasu suka rasa rayukan su wasu Kuma akayi garkuwa dasu.
Zaku iya karanta: gaskiya akan maganar nura Khalid
A yau talata me neman takaran shugabancin kasa a jamiyar APC bola tinibu ya ziyarci Nasiru Elrufa’i a gidan gomnati domin jajanta ma gomnatin kaduna da mutanen kaduna akan irin abubuwan da suke faruwa dasu usanman nakiyar da ta tashi da jirgin kasa a hanyar kaduna Abuja.
Bola tinibu dai ya fito kwanshi da kwar kwatan shi domin ganin ya samu shugabancin kasan Nan inda ya dade da nuna ra’ayin sa akan neman zama shugaban kasa inda ya nuna hakan wani tsohon kudiri ne da yake dashi tinda dadewa Amma gashi yanzu Yana ganin lokacin daya kamata yayi daya zama shugaban kasa.
Da yawan mutane dai suna ta fadin Albarkacin bakin su akan bola tinibu wasu suna ganin ya cancanta wasu Kuma suna ganin be cancanta ba saboda tsufa ko Kuma wani Abu na rashin lafiya.
Inme karatu be manta ba an Saka nakiyar me karfin gaske a hanyar jirgin kasa inda ta tarwatsa jirgi har wasu daga cikin mutanen suka jikkata wasu suka rasa rayukan su Inda wan nan hari me Muni ya Tayar da hankalin mutanen kaduna gaba daya musamman masu guje ma hanyar Mota suna Hawa jirgin kasa domin su samu tsaro na guje ma masu garkuwa da mutane.
Bayan faruwan wan nan fashewar nakiyar a titin jirgin kasa gomnati tarayya tayi tir da Allah wadai akan wan Nan Abu da ‘Yan ta’adda sukayi akan hanyar kaduna Abuja.
Amma dai dukda hakan talakawan Nigeria Basu gamsu da wan Nan tirr da Allah wadai da Gomnatin tarayya tayi ba ganin inda gomnati ta kama Hanu tayi shiru akan harkan tsaro Kamar bata damu da abinda yake faruwa da talakawan da sukayi ruwa sukayi tsaki don ganin ankafa wan Nan gomnati.
Wasu daga cikin talakawa sunyi anfani da karfin su da lafiyar su wasu ma harda kudin su inda sukayi ta siyan katin APC suna turawa domin tallafa ma APC ta samu mulkin kasa.
Inme karatu be manta ba kwanaki kadan baya malam nura Khalid yayi tsakaci aka abinda ke faruwa hakan yasa aka cire shi daga shugabancin limanci da yakeyi.