Safaran yaran mata yayi yawa Kuma yazo da sabon salo – NAPTIP
Fataucin yara yanmata masu kananan shekaru yayi yawa a Nigeria.
Hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) a jiya Larabar ta ce kusan kashi 60 cikin 100 na masu safarar mutane a Italiya ‘yan Najeriya ne kuma ta bayyana lamarin a matsayin abin ban tausayi kawai Kuma abin kunya ga Nigeria na kaurin suna akan wan Nan irin Hali na safaran mutane Wanda kowa yasan ba abune me kyau ba.
Director na Hukumar NAPTIP mai kula da horars da ma’aikata, Mista Orakwue Arinze ne ya bayyana hakan a yayin wani taro na kwanaki biyu mai taken Masu rauni, mabukata da wadanda rikicin cikin gida ya shafa ko Wanda iftila’i ya shafa wanda hukumar ta shirya tare da Joshuel Global Ventures Limited wanda aka gudanar a Sabon Gari. , Zaria, kaduna state.
Hukumar ta NAPTIP ta jagoranci wani taro don wayar da kan alumma musamman ma iyayen yara don nunar musu da illolin safarar mutane da cin zarafin mata ba ba abune me kyau ba hakan Yana Bata tarbiyan yara da jefa rayuwar su a Cikin hadari.
Arinze ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yi iya bakin kokarinta ta hanyar samar da wata doka a kasar nan a shekarar 2015 kan cin zarafin jama’a musamman yara da yanmata da kuma aikata laifin fyade da sauran lefukan cin zarafin danadam.
Ya kuma bukaci gwamnatocin jihohi da wasu daga cikin manyan mutane na kasar nan da su hada hannu da hukumar domin kawar da al’umma daga wannan annoba da yake adaban alumma na safaran kananan yara musamman mata.
Daraktan ya kuma yaba da kokarin wasu daga cikin manyan mutane a kasar nan da wasu daga cikin Yan siyasa akan kokarin da sukeyi wajen tallafa ma kana Nan yara da mata wajen karatu da Sana’a domin su tsaya da kansu ba tare da jiran wani ba.
Hakika in me karatu zai duba safaran yara mata a kasar nan tamu na Nigeria tayi yawa inda ake fita dasu kasashen waje wasu da sunan aiki, wasu aikin sukeyi wasu Kuma akasin hakan ne